Home Labarai Ciyar da Addinin Allah gaba hakkin dukkan Musulmi ne – Dr. Sani Rijiyar Lemo

Ciyar da Addinin Allah gaba hakkin dukkan Musulmi ne – Dr. Sani Rijiyar Lemo

0
Ciyar da Addinin Allah gaba hakkin dukkan Musulmi ne – Dr. Sani Rijiyar Lemo

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci dake jihar Kano, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yayi kira ga Musulmi da su ciyar da dukiyarsu domin daukaka addinin Allah da kuma taimakawa Musulmi.

Malamin yayi wannan kira ne a lokaciin da yake gabatar da karatun Tafsirin al’kurani da yake gabatarwa a masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake Kofar Gadonkaya a jihar Kano.

A yayin da yake bayanin taimkon addini, ya janyo ayoyin al’kurani da hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, da suka yi nuna da taimakon addini Allah da kuma daukaka kalmar Allah, inda yace wanda yayi haka zai samu lada mai yawa.

Haka kuma, Shehun Malamin yace bai kamata Musulmi yayi aikin da zai jefa rayuwarsa cikin matsala ba, inda yace “Kada Musulmi suyi sakaci wajen bibiyar abubuwan da zai sanya su sami nasara”.

“Kada ku bar ciyarwa don daukaka addinin Allah saboda kuna tsoron talauci” Yace duk kankantar abinda mutum yake da shi kada ya raina wajen taimakon addinin Allah.