
Kudirin dokar kafa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, Gwarzo, Jihar Kano, domin kula da harkokin kiwon lafiya da sauran al’amuran da suka shafi hakan, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Kudurin dokar, wanda Musa Garo (APC-Kano) ya gabatar a yau Laraba ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar ne a ranar 24 ga watan Maris.
Da yake jagorantar muhawarar, Garo ya ce kudurin dokar ya nemi a samar da tsarin doka na kafa cibiyar don bunkasa da gudanar da kiwon lafiya don bukatun al’ummar mazaɓarsa da ma jihar baki ɗaya.
A cewarsa, Ƙaramar Hukumar Gwarzo a jihar Kano na matukar bukatar wannan asibitin da ake shirin samarwa, yana mai cewa a halin yanzu mazauna yankin na fama da ƙarancin harkokin kiwon lafiya .
“Ƙudirin ya bukaci samar da kayan aiki, kulawa da kuma sarrafa cibiyar kiwon lafiya ta yadda za a samar da kayan aiki don gano cutar, magani da kuma ayyukan gyarawa.
“Don ginawa, ba da kayan aiki, kulawa da sarrafa cibiyar tare da ingantattun ma’aikata, masu fasaha, likitoci da ma’aikatan jinya.
“Don samar da manyan manufofi da jagororin da suka shafi manyan shirye-shiryen fadada cibiyar kiwon lafiya da kuma samar da kayan aiki don horar da daliban likitanci na cibiyoyin haɗin gwiwa,” in ji shi.
Garo ya ce idan aka kafa cibiyar, ba wai kawai za ta ɗinke ɓarakar da ke tattare da rashin wanzuwar cibiyoyin kiwon lafiya a Gwarzo ba, har ma za ta haɓɓaka kiwon lafiya ga jihohin da ke maƙwabtaka da jihar ta Kano.