
Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce ya na bada Naira miliyan 30 a kowace rana ga kowane reshe na bankunan da ke jihar Bauchi, domin kara samun damar baiwa kwastomomi sabbin takardun kudi.
Abdulkadir Jibrin, jami’in babban bankin ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke sa ido a kan bankunan a Bauchi a jiya Litinin domin tabbatar da samun sabbin takardun kudi na naira ga mazauna jihar.
Ya ce makasudin gudanar da atisayen shi ne don tabbatar da samun sabbin takardun kudi na Naira a bankuna da kuma samun saukin musanya tsofaffin takardun kudi da sabbi da aka sake yi wa mazauna jihar.
“N10,000 da kasa da haka za a iya musayar kowane mutum kuma idan adadin ya wuce haka sai a bude jakar banki.
“Kullum kowane reshe a fadin jihar nan na karbar Naira miliyan 30 don tabbatar da cewa na’urorinsu na ATMs sun cika da kudin domin mutane su cire,” inji shi.
Sai dai ya bukaci jama’a da su yi amfani da tsawaita wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabarairu su ajiye tsoffin kudadensu a bankuna domin gujewa hasarar kudi.