
Ana iya cewar tsugunne bata karewa uwar jam’iyyar PDP ba, domin yau an kuma samun wasu da suka kaddamar da sabuwar jam’iyyar PDP a babban birnin tarayya Abuja, a cewarsu ba zasu bi ‘Unity list’ din da aka kakaba musu ba.
Sabuwar sakatariyar PDP din dai na nan akan titin Tito Broz daura da titin Jimmy Carter. Sabon shugaban ‘yan a ware na PDP din Emmanuel Nwosu shi ne ya sanar da hakan yau a Abuja, a lokacin da yake kaddamar da sabuwar sakatiyar PDP din.
Su dai wadannan ‘yan Aware din a binciken DAILY NIGERIAN HAUSA, fusatattun magoya bayan wani bangare ne da suka sha kaye a zaben da ya gabata a ranar 9 ga watannan a birnin tarayya Abuja.
Sabon shugaban ‘yan Aware na PDP din Nwosu, yace kasancewar Uche Secondus a matsayin Shugaban jam’iyyar Damfara ce kawai da aka yiwa jam’iyyar, domin kuwa a cewarsa, an sabawa dukkan tabbatattun ka’idojin zabe wajen kakabawa mutane Secondus.
Idan ba’a manta ba, a satin da ya gabata, Gwamnan jihar Bayelsa ya jagoranci kwamitin sasantawa da duk mutanan da suke ganin anyi musu ba daidai ba a jam’iyyar sakamakon wannan zabe da aka yiwa Uche Secondus.
Ko ya zata kaya, zamu ji.