
Daga Hassan Y.A. Malik
Kungiyar kwadago ta kasa, (NLC), reshen jihar Jigawa ta raba bashin shinkafa fiye da bahu 21,000 ga ma’aikatan jihar dana kananan hukumomi da kuma malaman makaranta don rage wa mambobinta radadin tsananin babun da a ke ciki musamman ma a wannan lokaci na azumin watan Ramadana.
Shugaban kungiyar reshen jihar Jigawa, Comrade Usman Ya’u Dutse ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishinsa.
Ya ce gwamnatin tarayya ce ta baiwa jihar Jigawa kason shinkafa buhu dubu talatin domin sayarwa ga al’umma akan farashin naira dubu goma sha biyu kan kowane buhu.
Comrade Usman Ya’u Dutse, ya kara da cewar Gwamna Badaru Abubakar ne ya biya kudin shinkafar a madadin ma’aikata.
Ya ce an raba shinkafar ne ga ma’aikata a cibiyoyi biyar da aka ware da suka hadar da: Gumel da Dutse da Ringim da Kazaure da kuma Hadejia.
Shugaban kungiyar kwadagon ya kara da cewar za a yanki kudin shinkafar ne a cikin albashin ma’aikata na watan Mayu da kuma Yuni yayin da za a kawo ragowar shinkafar buhu dubu takwas nan bada jimawa ba.
Ya ce baya ga shinkafar, kungiyar zata kawo sauran kayayyakin masarufi da za a sayarwa maaikata a farashi mai sauki