Home Labarai Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami’ar Maitama Sule

Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami’ar Maitama Sule

0
Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami’ar Maitama Sule

Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Yusuf Maitama, reshen Kano, ta koka kan rikicin da ke shirin kunno kai, idan har gwamnatin jihar ta gaza magance bukatunta.

Kungiyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta shafe watanni tana yin watsi da bukatunsu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban reshen da kuma sakataren kungiyar Mansur Sa’ id da Yusuf Gwarzo suka sanya wa hannu a yau Alhamis a Kano.

Ya ce bukatunsu guda uku ne wadanda suka hada da inganta yanayin aiki ga mambobinsu.

Sauran kuma sun haɗa slda bunƙasawa da kuma hanzarta samar da ci gaban jami’ar ta hanyar bayar da kuɗaɗen aiki mai ɗorewa, ƙarfafawa da kare ikon cin gashin kai na jami’a da ƴancin ilimi.

Kungiyar ta ce ba ta so ta baiyana yanayin a fili ba amma kokarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin ta biya musu bukatunsu ya ci tura.