Home Labarai Kungiyoyin Mata sun sayawa Mansur Manu Soro takardun shiga zabe

Kungiyoyin Mata sun sayawa Mansur Manu Soro takardun shiga zabe

0
Kungiyoyin Mata sun sayawa Mansur Manu Soro takardun shiga zabe

 

Kungiyoyin mata dake kananan hukumomin Ganjuwa da Darazo da kuma abokan huldar kasuwanci musamman masu gidajen mai a Jihar Bauchi sun had’a taro da sisi sun sayawa mai tallafawa Gwamna M A Abubakar akan kungiyoyin da bana Gwamnati ba da abokan kawo cigaba Alhaji Mansur Manu Soro form d’in tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Darazo/Ganjuwa.

Da yammacin yau wadannan kungiyoyi suka shirya wani gangami na musamman domin mik’a wannan form gareshi a garin Soro na Karamar Hukumar Ganjuwa. Kungiyoyin matan sun hada da:

1.NASIHA WOMEN’S DEVELOPMENT ASSOCIATION SORO GANJUWA EAST, GANJUWA L. G. A

(2)-GANJUWA WOMEN’S ASSOCIATION FOR THE DEVELOPMENT OF PEACE AND DEMOCRACY,GANJUWA L. G. A

(3)-ABASAMA AQUAZITION CENTRE DARAZO L. G. A

(4)-JARUMTA SADE DISTRICT WOMEN’S DEVELOPMENT ASSOCIATION DARAZO L. G. A

Hajiya Fatsuma Baba Hamza da Malama Amina Abubakar ne sukayi jawabi amadadin kungiyoyin matan inda suka ce sunyi wannan sadaukarwa ne domin sakayya ga irin namijin kokarin da yayi wajen gudanar da ofishinsa da kuma yadda ya taimaka wajen inganta rayuwar mata bama a Ganjuwa da Darazo ba harma da Jihar Bauchi gaba d’aya. Sun ce lallai suna da yak’inin in har Mansur Manu Soro ya tafi majalisar wakilai al’uma zata amfana da romon dimokradiyya ta kowanne bangare kasancewar an gwada shi an gane na k’warai ne.

Shima da yake jawabi a madadin abokan kasuwancin Alh Mansur Manu Soro Alh Aliko Shehu Muhammad (MD Infinite Oil & Gas) yace irin kwatanta gaskiya da rik’on amana da mutunta mutane na Mansur Manu Soro ne yasa suka bada wannan gudunmawar.

Da yake maida jawabi, mai gayya mai aiki Alh Mansur Manu Soro ya nuna matukar godiyarsa marar adadi bisa wannan karamci da kungiyoyin matan da abokan kasuwancinsa suka masa. Ya tabbatar musu da cewa ya amshi wannan form kuma zai shiga takara. Ya bayyana cewar wannan takara da zaiyi bata kashin kansa bace ta al’umar Ganjuwa da Darazo ne da suka rika kiransa ba dare ba rana ya fito wannan takara domin kawo cigaba a yankin. Alh Mansur ya tabbatarwa da al’uma cewa ba zai basu kunya ba kuma zai matukar ya lashe zaben zai kawo shirye-shiryen cigaban al’uma da yankin bai taba samu ba.