Home Labarai Kuri’arka ‘yancinka

Kuri’arka ‘yancinka

0
Kuri’arka ‘yancinka
Yasir Ramadan Gwale, mai sharhi kan al'amuran siyasa a jihar Kano

Daga Yasir Ramadan Gwale

Yana da kyau mutane su sani su kuma fahimta cewar kowanne mutum a Najeriya kuri’a daya gareshi, kuma wannan kuri’ar itace ‘yancika idan har mun mallaketa. Ina samun kaina cikin matukar mamaki idan naga mutum mai ilimi ko wani wanda ya san me yake yi yana fadin shi ya dena zabe, ko shi ba zai yanki katin zabe ba.

A yanzu da abubuwa suka bayyana a zahiri, bai kamata ace ana samun masu irin wannan gurguntaccen tunani ba. Ya kamata mu sani, batun katin zaben nan fa yana da alaka da rayuwarmu da ta ‘ya ‘yanmu da jikokinmu, domin da wannan katin zabe ne zamu zabi Shugabanni, su kuma Shugabannin nan, su ne mas’uliyyar gudanar da al’amuranmu yake a wuyansu.

Na san da dama wasu zasu yi zargin cewar ai mun gwada a baya mun gani, abinda muka zaba ba shi ne abinda ake bamu ba. Wannan ba zai iya zama dalili daga cikin dalilai da zasu hana mutumyankar katin zabe da kuma yin zabe ba. Lallai a halin da muke ciki yana iya zama wajibi a garemu kowanne baligi da ya yanki katin zabe kuma ya tabbatar yayi zabe inda yana da lafiya a lokacin zabe.

Yana da kyau mu kara sani cewar, da kuri’ata da taka da tasu za’a a hada a kirga ace daya biyu har zuwa miliyan.Ta hanyar zabe ne da kuma wayar da kai kadai zamu iya samun Shugabannin da muke so da zasu gudanar da al’amuranmu. A cikin miliyoyin mutanen da suke wannan kasar, mutum guda ne kadai zai iya zama Shugabanmu, kuma ta hanyar zabe zamu zabe shi.

A wannan lokaci da muke fama da magauta da ‘yan bora da kuma makiya na kusa da na nesa. To mu sani duk yawan da muke alfahari da shi, matukar bamu yanki katin zabe kuma mun fita mun yi zabe ba, to yawan ya tashi a banza, kuma mun zama taron tsintsiya babu shara.

Ya zama wajibi a garemu, mu sani yawanmu a zahiri shi ne yawan kuri’unmu. Ina amfanin muna ikirarin yawan al’umma a wannan bangaren namu, amma anje wajen zabe an mana fintinkau? Yawan ya zama yawan da bai mana amfani ba tunda an sha gabanmu.

Mu sani magautanmu, kullum hudubarsu shi ne su yanki katin zabe kuma su fita su yi zabe, domin su kamo yawan kuri’unmu, sabida sun fahimci tunaninmu na rashin son yankar kain zabe. Lallai ne muma mu sani duk wani matashi da ya kai matsayin zabe to lallai ya fita ya yanki katin zabe, kuma ya tabbatar yafita yayi zabe lokacin zabe.

Zarge zargen da muke yi a lokacin zabe, na hanamu abinda muka zaba, ko sace mana zabe, ko kawo yamutsi a lokacin zabe, galibi duk suna faruwa ne sakamakon rashin yankar katin zabe da mutane masu ilimi da tarbiyya da dama da basu yi ba, wannan ce takan baiwa batagari daga cikinmu sukan ci karensu babu babbaka a lokacin zabe, suma kuma sabida basu san kansu bane, basa tunanin makomarsu da ta ‘ya ‘yansu shekaru 30 ko 50 nan gaba.

Duk wani mai hankali kuma mai tunani, da yake kallon kasarnan, idan har bamu dage mun tashi tsaye ba akan batun zabe da kuma zabar mutane na gari. To wallahi za’a cigaba da rayuwa ne kashin dankali a kasarnan, domin kuwa masu arziki zasu yi ta samun arziki su da ‘ya ‘yansu, talakawa kuwa zasu yi ta shan wahala su da ‘ya ‘yansu, kusan yanzu alamu suna nuna cewar, indai kai talaka ne to ‘ya ‘yanka da jikokinka duk talakawa zasu kasance, haka in kai ami ilimi ne ko wani mai arziki haka zuri’arka zasu kasance.

Sauya wancan tsari na gadar talauci ko arziki yana da alaka da tsayawarmu da kuma jajircewarmu wajen ganin mun gayawa kanmu gaskiya kuma mun yiwa kanmu kiyamul laili mun yanki katin zabe mun kuma tabbatar mun yi zabe. Wannan batun zaben ko mu sani ko kada mu sani yana damfare da rayuwarmu da ta ‘ya ‘yanmu. Jama’a mu fita mun yanki katin zabe, sannan mu zabi mutanan kirki lokacin zabe. Kuri’arka ‘yancinka.