
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a Jihar Legas, ta ce alkaluma sun nuna cewa a halin yanzu, jihar na da masu rajistar zaɓe kimanin miliyan bakwai.
Kwamishinan Zaɓe na INEC, REC, a jihar Legas, Olusegun Agbaje, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a yau Lahadi.
A cewarsa, idan har ya zuwa yanzu an kara adadin sabbin masu rajista a ci gaba da aikin yin katin zaɓe, CVR, ga wadanda ke cikin rajistar masu kada kuri’a a da a jihar, adadin zai kai kusan miliyan bakwai.
“A jihar Legas, ya zuwa ranar Litinin 18 ga watan Yuli, wadanda suka yi rajista ta yanar gizo sun kai 640, 560 amma da yawa daga cikinsu ba su kammala rajista ba. Wadanda suka kammala yin rajistar sun kai 451,156.
“Jimillar wadanda suka yi rajista a jihar Legas kafin a fara aikin CVR da ke gudana ya kai 6,570,291, kuma idan muka kara da sabbin masu rajista, muna da masu kada kuri’a kusan miliyan bakwai,” in ji Mista Agbaje.