Home Labarai Kusan yara miliyan 2.2 ne su ka fuskanci barazanar talauci a Jamus

Kusan yara miliyan 2.2 ne su ka fuskanci barazanar talauci a Jamus

0
Kusan yara miliyan 2.2 ne su ka fuskanci barazanar talauci a Jamus

Jamus ta sanar da cewa kusan yara miliyan 2.2 na da matasa ƴan kasa da shekaru 18 su ka fuskanci barazanar talauci a 2022, wanda ya yi daidai da haɗarin samun kashi 14.8 cikin ɗari.

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa, a yau Laraba ta bayar da rahoton cewa, yadda yara da matasa ke fuskantar barazanar talauci, ya danganta ne da ilimin iyayensu, da dai sauransu.

A cewar hukumar, hadarin da ke tattare da yaran da iyayensu ke da karancin ilimi, kamar takardar shaidar kammala sakandare a matsayin mafi girman cancantar su ya kai kashi 37.6 cikin 100 a 2022.

Sabanin haka, kawai kashi 14.5 cikin 100 na yan kasa da shekaru 18 tare da iyayen da ke da matsakaicin matakin ilimi suna cikin haɗarin talauci.

Wannan rukunin ya haɗa da iyaye masu shaidar kammala karatu kamar kammala karatun sana’a ko ki jarrabawar sakandare.

Kashi 6.7 ne cikin 100 na yaran da iyayensu suka sami ilimi mai zurfi kamar digiri na jami’a – ke cikin hadarin talauci.

A cikin 2022, wannan adadi ya kasance € 1,250 ($ 1,384) ne mutum ke samu a kowane wata ga mutumin da ke zaune shi kaɗai a Jamus da kuma € 2,625 net kowane wata ga manya biyu masu yara biyu ‘yan ƙasa da shekara 14.