
Gwamnatin jihar Kaduna a yau Laraba ta ce a kwai cikakken tsaro a titin Kaduna zuwa Zariya, saɓanin ikirarin raɗe-raɗin rashin tsaro da a ke yi a hanyar.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Ya ce saɓanin jita-jita maras tushe, hanyar lafiya lau take kuma ba ta da wata matsala ga matafiya, inda ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
Aruwan ya ce an ja hankalin gwamnatin Kaduna kan sakon da ake yadawa, inda ake shawartae ƴan jihar da kada su shiga ko fita daga Zariya, sannan a ka yi zargin cewa akwai daruruwan ‘yan bindiga a Dumbi da Jaji a kan hanyar zuwa Zariya.
“Gwamnatin jihar Kaduna na fatan karyata wannan sakon, kuma tana kira ga al’umma da su yi watsi da shi gaba daya. Ƙoƙari ne na zahiri don haifar da tsoro.
“Gwamnatin jihar Kaduna tana tabbatar wa da al’umma da matafiya cewa hanyar Kaduna zuwa Zariya ba ta da haɗari.
“An yi kira ga mazauna garin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, kada su yarda da rahoton karya,” in ji Mista Aruwan.