
Hukumomin kwalejin kimiyya da fasaha ta Auchi sun kori dalibai 40 bisa samun su da laifin bada sakamakon jarabawa na bogi da kuma gaza cika wasu ka’idojin shiga makarantar.
Jami’iar hulda da jama’a ta makarantar, Adebola Ogunboyowa, a cikin wata sanarwa ga manema labarai, ta ce an kori daliban ne biyo bayan sakamakon aikin tantance daliban da aka saba yi na zaman karatun zangon 2020/2021.
Ta ce daliban da aka kora sun rabu a sassa daban-daban na makarantar.
Ta ce an kama daliban da abin ya shafa da laifin bada sakamakon jarrabawa na jabu domin samun damar shiga shirin Diploma n’ta kasa (ND) da kuma Babbar diploma, wato Higher National Diploma (HND).
Ta kuma bayyana cewa shugaban cibiyar, Dakta Salisu Umar ya gabatar da sabbin karaturruka guda 12 da za a fara a wannan zango na karatu na 2022/2023.
Ta jera kwasa-kwasan kamar haka: Fasahar Buga Hotuna, Walda da Fasahar Ƙere-ƙere, Koyon Safarar Kayayyakin Kasuwanci, Ilimin Labirare da Fasahar Sadarwa, da sauran su.