Home Labarai Kwalin digiri ya fara daina amfani wajen bada aiki a Nijeriya — Rijistaran JAMB

Kwalin digiri ya fara daina amfani wajen bada aiki a Nijeriya — Rijistaran JAMB

0
Kwalin digiri ya fara daina amfani wajen bada aiki a Nijeriya — Rijistaran JAMB

Farfesa Ishaq Oloyede, Rijistaran hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ya bayyana cewa, yanzu babu tabbacin cewa Digiri zai yi amfani wajen samun aiki, sai dai kawai wani kwali na nuna cewa an yi karatu.

Oloyede ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a lokacin da yake gabatar da laccar bikin yaye ɗalibai ta 10 da ta 11 a Jami’ar Jihar Kwara, Malete.

Ya ce: “Kammala karatun digiri ba wai kawo karshen karatu ba ne, a’a mafarin koyo ne da kuma mabudin rayuwar jami’a.

“Wadanda za su iya koyo, da sake koyo da kuma kammala koyo su ne wadanda za su kare da nadama.

“Sabbin damammaki za su fito a fannin fasaha na zamani kuma za a buƙaci fasaha da yawa waɗanda ba a yi tunanin su ba a makarantun gargajiya.

“Kwalin digiri ba shi da tabbacin samar da aiki yanzu,” in ji magatakardar JAMB.