
Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Kano mai ritaya, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce babban ƙalubalensa shi ne kotuna da ke bayar da belin waɗanda ake zargi da aikata laifuka bayan an gurfanar da su a gaban kuliya.
Ya bayyana haka ne a jiya Litinin a wurin taron masu ruwa da tsaki na ƴan sanda a Kano.
“Zan yi ritaya daga aikin rundunar ‘yan sandan Nijeriya a ranar 27 ga Yuli, 2022, bayan na cika shekara 60 a duniya.
“Babban kalubale na a harkar ‘yan sandan jihar Kano shi ne bayar da belin masu laifi bayan an gurfanar da su a kotu.
“Mun kama mutane da yawa da ake zargi da aikata manyan laifuka kamar fashi da makami da kuma satar motoci.
“Amma nan da nan, sai mu sake kama su da irin wannan laifin bayan mun gurfanar da su a gaban kotu a baya.
“Saboda haka, ina kira ga wadanda abin ya shafa da su yi abin da ya kamata wajen tabbatar da hukuncin da ya dace ga masu laifi,” in ji shi.