
Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Tilde ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.
Tilde, wanda ya sanar da murabus dinsa a shafinsa na Facebook, ya ce ya aike wa Gwamna Bala Mohammed takardar murabus din.
Kwamishinan ya ce murabus din ya zama dole domin halartar kiran wani abokin aikinsa da ke matukar bukatar ayyukan sa.
Ya ce: “A ‘yan mintoci da suka gabata, yau 5 ga Disamba, 2022, na samu takarda daga sakataren gwamnati ta mika sakon saki na da mai girma gwamna ya yi.
“A don haka, Sakataren ya gabatar da godiya daga Gwamnan Jihar bisa gudunmawar da ka ke bayarwa a fannin Ilimi da kuma yi maka fatan alheri a cikin ayyukanka na gaba…”
“Da wannan ne wa’adina na Kwamishinan Ilimi ya zo karshe. Na yi farin cikin ganin ƙarshen abin da ya kasance mai wahala amma shekaru masu amfani kuma zan kasance da godiya ga Allah wanda ya tsaya mini har zuwa minti na ƙarshe.”