
Kwamishinan Kuɗi da Cigaban Tattalin Arziki na Jihar Kano, Shehu Na’allah ya sauya sheƙa da ga jam’iyar APC mai mulki zuwa NNPP.ì
Na Allah ya sauya sheƙar ne a yau Laraba tare da tsohon ubangidan sa, Sanata Ibrahim Shekarau.
Nan take kuma a ka damƙa mishi takarar Majilisar wakilai a mazaɓar Kura/Madobi/Garun Mallam.