
Akalla mutane dubu ɗaya da dari biyu da hamsin ne za su ci gajiyar bada magani kyauta, a wani ɓangare na bikin cikar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 66 da haihuwa.
An tsara shirin bada maganin ne domin karrama babban jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Za a bada maganin ne kyauta ga mutane masu kananan cututtuka.
Ƙungiyar Malaman Kwankwasiyya, karkashin jagorancin Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata da sauran kungiyoyin tallafi, karkashin kungiyar Kwankwasiyya Concern Forum da Kano Lafiya Jari Initiative ne suka shirya taron.
Daya daga cikin wadanda suka shirya taron, Abdullahi Tarauni ya ce sun bayar da tallafin magunguna na miliyoyin naira domin tabbatar da cewa mutane da dama sun samu maganin ba tare da ko sisi ba.
Sama da ma’aikata 50 ne aka tura domin gudanar da shirin, wadanda akasarinsu cikin wadanda suka amfana da tallafin karatu na Kwankwaso ne a lokacin yana gwamnan Kano da ma bayan nan.