
Tsohon wakilin mazaɓar Sumaila da Takai a Majalisar Wakilai, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ƴan Kwankwasiyya da PDP da ma G7, wato ɓangaren su Sanata Ibrahim Shekarau sun fara tuntubarsa domin ya koma cikin su.
Kawu Sumaila, ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi ta kai-tsaye, ta tsawon sa’a 2, da yayi da wasu gidajen rediyo a Kano a jiya Lahadi da daddare.
Kawu Sumaila, wanda tsohon hadimin Shugaban Ƙasa ne s fannin Majalisar Wakilai, ya ce mafi yawa daga cikin magoya bayansa su na da fargabar abun da ya faru a2019 zai iya sake faruwa a kakar zaɓe ta bana, inda ya ƙara da cewa, don haka su ke ba shi shawarar ya fice da ga jam’iyyar APC.
” Tun daga abun da ya faru a taron ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar APC na Kano-ta-Kudu, magoya baya na su ka fara zaton ko baza a yi mana adalci ba. Amma dai na faɗa musu cews shi Gwamna uban kowa ne, kuma ban ga abun aibu ba Idan ya Isar da saƙon wani”. Inji Kawu Sumaila.
Kawu ya ƙara da cewa ya faɗa wa magoya bayansa cewa, shugabanni da masu ruwa da tsaki a APC sun ba shi tabbacin za su bari demokaradiyya ta yi aikinta, ta hanyar masalaha ko kuma zaɓe.
Kawu, wanda a yanzu haka ya ke takarar kujerar Sanatan Kano-ta-Kudu, ya baiyana cewa tuni ƴan G7 da ƴan Kwankwasiyya da ke jam’iyyar NNPP dama yan jam’iyyar PDP “duk su ka fara neman na je muyi siyasa. Su na kira na ne da na je domin sun san Ina da jama’a.
“Duk wanda ya ke son cin zaɓe a Kano dole ya nemi ƴan siyasa irina ba waɗanda ba su iya shiga cikin mutane ba. Sun kasa zuwa garinsu, sai zabe ya zo su ɗauko kuɗi su taho za su sayi delegate, tunda sun mayar da su kamar ragunan layya wanda shi ake saya ranar kuma a yankashi ba sai an Sha wahala ba”.
A zaben Shekara ta 2019 dai kawu Sumaila ya fito takarar Sanatan Kano-ta-Kudu, Inda su ka kara da Sanata mai ci yanzu, Kabiru Ibrahim Gaya, kuma a wannan karonma yace zai sake jarrabawa a jam’iyyar su ta APC.