Home Labarai Kwankwaso ya ƙaddamar da ayyukan ci-gaba a Kaduna

Kwankwaso ya ƙaddamar da ayyukan ci-gaba a Kaduna

0
Kwankwaso ya ƙaddamar da ayyukan ci-gaba a Kaduna

A yau Juma’a ne tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da sabuwar Kasuwar Ungwan Rimi da kuma titin Makaranta da Emir Road a Kaduna bisa gayyatar gwamna Nasir El-Rufai.

Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, shi ma ya kaddamar da titin Bida da aka karawa fadi, wanda ke cikin shirin sabunta birane na gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai.

Akande l, wanda ya kaddamar da hanyar a madadin Lai Mohammed, ya yabawa El-Rufai kan sauya fasalin Kaduna don amfanin al’umma.

Ali Modu Sheriff, wanda ya kaddamar da gadar sama ta Kabala da ke hanyar Aliyu Makama, Barnawa, ya ce ya yi imanin cewa mutanen Kaduna za su tuna da abubuwan alheri da El-Rufai ya yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wanda ya kaddamar da hanyar Raba, ya ce aikin na alheri ne da ci gaban al’ummar jihar Kaduna.

Gwamna El-rufai, a wajen kaddamar da ayyukan, ya ce ayyukan wani bangare ne na kokarin da gwamnatinsa ke yi na fadadawa da inganta muhimman ababen more rayuwa a fadin jihar ta hanyar shirin sabunta birane.

El-Rufa’i ya yi nuni da cewa, ayyukan wani muhimmin ci gaba ne ga jihar domin suna taka rawar gani wajen hada kan al’umma da jawo jari da kuma bunkasar tattalin arziki.