
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya ji raɗe-raɗin da a ke yi na cewa Sanatan Kano ta Tsakiya, Mallam Ibrahim Shekarau na shirin ficewa daga jam’iyar zuwa ta PDP.
Da ya ke zanta wa da BBC Hausa a yau Laraba, Kwankwaso ya ce idan jam’iya ta girma kamar NNPP, to ba makawa sai an samu cecekuce a cikin ta.
A cewar Kwankwaso, batun cewa na jikin Shekarau sun koka a kan ba cika musu alkawuran da a kai musu ba, sai shi Shekarau ɗin ne kaɗai a ka cika masa nasa ba gaskiya ba ne.
Kwankwaso ya fayyace cewa, lokacin da mutanen Shekarau su ka miko bukatunsu na takara, an riga an kammala zaɓukan fidda-gwani kuma kowa ya samu gurbin takara.
Ya ƙara da cewa sai yai musu bayani cewa ba za ta yiwu a biya musu bukatunsu na takara ba sabo da sun miko su ke bayan an riga an kammala raba guraben takarar.
“Sai mu ka yi musu bayani cewa su bari idan aka ci zaɓe, tunda mu na sa ran za mu kafa gwamnati a 2023, sai a ga guraben muƙamai da su ka dace a basu,” in ji Kwankwaso.
“Ba ka raba jam’iyya da cecekuce musamman in ta girma kamar NNPP. Nima na ji wannan magana amma gaskiya babu wata yarjejeniya da a kai da ta wuce bukatu da a ka kawo kuma mun gama sai aka kawo wasu bayan an riga an kammala komai.
“Bukatun na takara ne kuma an riga an raba takara. Sai dai mu jira idan aka kafa gwamnati sai kuma a shigar da kowa tunda muna jiran lokaci ne kawai.
” San da suka kawo bukatun ƴan takara an riga an raba takarar an kammala zaɓuɓɓuka. Magana ce ta wasu su sauka wasu su maye gurbinsu, kuma hakan wahala ce da shi,” in ji Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano.
Tsohon Sanatan kuma ya ƙara da cewa shi tsarin Kwankwasiyya babu rufa-rufa a ciki, tsari ne a buɗe.
Ya kuma tabbatar da cewa babu wata matsala tsakanin sa da Shekarau, in da ya ƙara da cewa “amma in sha Allah idan mu ka ci zaɓe, to za mu rabawa kowa muƙamai.”