Home Labarai Kwankwaso ya magantu kan ziyarar ta’aziyya da Ganduje ya kai masa

Kwankwaso ya magantu kan ziyarar ta’aziyya da Ganduje ya kai masa

0
Kwankwaso ya magantu kan ziyarar ta’aziyya da Ganduje ya kai masa

 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya baiyana cewa ziyarar da abokin burmin sa na siyasa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai masa kan ta’aziyyar rasuwar ƙanin sa, abin farin ciki ne da jin daɗi.

A jiya Talata ne dai Daily Nigerian Hausa ta rawiato cewa Ganduje ya yi tattaki zuwa dangin Kwankwaso a Ƙaramar Hukumar Madobi, sannan ya taso takanas-ta-kano zuwa gidan Kwankwason domin yin ta’aziyyar rasuwar Inuwa Musa Kwankwaso, ƙani ga tsohon gwamnan.

Ziyarar ta Ganduje ita ce karo na farko tun bayan da rikicin siyasa ya raba zumunci tsakanin tsofaffin abokan siyasa biyun jim kaɗan bayan an yi zaɓen gwamna na shekarar 2015.

Bayan Ganduje ya kai ziyarar ne sai BBC Hausa ta yi hira ta musamman da Kwankwaso, inda ya nuna cewa ziyarar gwamnan abin jin daɗi ce gare shi da kuma al’umma baki ɗaya.

“Tabbas ziyarar sa abin farin ciki ne da murna da jin daɗi ga ni kaina da al’umma baki ɗaya.

“Mu ba ma siyasa don gaba da keta mutuncin wani. Ba za ta yiwu ka zauna waje ɗaya kana ta sukar wasu cewa basu iya ba kai kuma ka ƙi shiga siyasa domin ka kawo gyara, wannan shine dalilinsa na shiga siyasa.

Da a ka tambayi Kwankwaso ko ziyarar ta gaisuwa da roƙon iri ce, sai ya kada baki ya ce, idan ma hakan ne ba abin mamaki ba ne, amma dai ziyarar za ta sanya farin ciki a zukatan al’umma.

Ya ƙara da cewa, “ai idan shugaba ya na yin ba daidai ba, a ka nuna masa cewa ba daidai bane amma bai yadda ba sai daga baya ya fahimta ya kuma gyara, to wannan ina ganin ba matsala ba ce,”

Kwankwaso ya kuma tabbatar da cewa babu wata tattaunawa ta ƙarƙashin ƙasa da ya yi ko ya ke yi da Ganduje, inda ya ce ” Kawai dai duk wanda ya ke shugaba ya kamata ya gane cewa ya fahimci abinda ya ke na daidai da ba daidai ba. Tun da farko ya kamata mutum ya fahimci ya na yin ba daidai ba, amma dai idan ya gane tun da farkon ko a tsakiya ko sai a karshe, to ba laifi ba ne, ya kamata dai a gyara,”

A yan kwanakinnan dai al’amuran siyasa a jam’iyyar APC na ci gaba da tabarbarewa, musamman ma rikicikin da ke tsakanin tsagin gwamnan da na Malam Ibrahim Shekarau.

Ko da yake anji gwamnan ba sau ɗaya ba ya na cewa matukar aka nemi a sulhunta to shi a shirye yake yayi sulhu da duk wadanda aka batawa.