
Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kammala digirin-digirgir, wanda a ka fi sani da PhD, ko Dakta, a Jami’ar Sharda da ke India.
A jiya ne Kwankwaso, tsohon Sanata, ya wallafa a shafinsa na facebook, inda ya nuna godiya ga Allah bisa samun wannan nasara.
Bayanin da Kwankwason ya wallafa ya nuna cewa ya samu digirin ne a fannin fasahar ruwa.