Home Kanun Labarai Kwankwaso ya fasa zuwa Kano

Kwankwaso ya fasa zuwa Kano

0
Kwankwaso ya fasa zuwa Kano

Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, Sanata mai wakiltar tsakiyar Kano a majalisar dattawa ta kasa, a ranar litinin ya bayyana jingine shirinsa na zuwa Kano a gobe talata, zuwan da aka jima ana cece-kuce akansa.

A lokacin da yake magana da manema labarai ta hannun tsohon sakataren gwamnatin Kano, Rabiu Bichi, yace,Kwankwaso ya jingine baun zuwan nasa Kanoa gobe sabida kiraye kiraye daga manyan mutane na ya jingine batun zuwan nasa.

Haka kuma, a cewar wani masanin kwakwaf, Kwankwason ya jingine baun zuwan nasa Kano ne, bayan da aka bukaci ganinsa cikin gaggawa a fadar Shugaban kasa, inda zai yi wata ganawa ta musamman tsakaninsa da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo.

Da yawa na ganin, wannan kira da akaiwa su Kwankwanso fadar Shugaban kasa, yana da akala da batun tsaro yayin wannan ziyara da Kwankwason yake son kaiwa Kano, domin za’a samu mummunar kafsawa tsakaninmagoya bayansa da na Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, idan za’a iya tunawa, a ranar juma’a, kwamishinan ‘yan sanda na jihar kano ya shawarci Kwankwaso da ya jingine batun zuwansa Kano a wannan lokacin.

A wata ganawa da yayi da manemalabarai, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Rabiu Yusuf, ya bayyana cewar, Kwankwaso yana da ‘yanci ya shigo Kano a ko da yaushe, yace amma rahotannin da suke samu, idan ya shigo ta za’a samu matsalolin tsaro a jihar.

Haka kuma, Kwankwaso ya nuna babu gudu babu ja da baya kan batun zuwansa Kano a gobe talatar, inda yace, duk abinda ya faru na tsaro a jihar, to kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabiu Yusuf ne ke da alhakin komai.

A lokacin da yake magana da manema labarai ta hannun tsohon sakataren Gwamnatinsa, Rabiu Bichi, a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana cewar, Kwamshinan ‘yan sandan jihar kanon ya shigar da kansa cikin al’amuran siyasar jihar, ta hanyar goyon bayan gwamna Ganduje.

Yace, Kwamishinonin Gwamnain Ganduje guda biyu, are da wani Abdulmajid Danbilki Kwamanda sun sha alwashin yin duk mai yuwuwa wajen hana Kwankwason shigowa Kano.

Haka nan shima Musa Iliyasu Kwankwaso ya shiga gidajen radiyo da dama a cikin birnin Kano inda ya dinga gabatar da shirin kai tsaye, yana bayyana cewar zasu yi amfani da karfi wajen hana kwankwaso shigowa kano, kuma yace duk sanda ya shirya zai shigo suma zasu shirya taro a ranar.

Haka kuma, “A wani faifan bidiya da ya yadu a shafukan sada zumunta na intane, an jiyo Abdullahi Abbas Sunusi yana maganganun tashin hankali akan batun zuwan na Kankwaso, inda yae nuna zasu baiwa matasa umarni su yiwa Kwankwason jifan Shaidan idan yazo kano” A cewar Rabiu Bichi.