Home Labarai An kwantar da mutane 120 a asibiti sakamakon shaƙar gurɓataccen sinadari a Kano

An kwantar da mutane 120 a asibiti sakamakon shaƙar gurɓataccen sinadari a Kano

0
An kwantar da mutane 120 a asibiti sakamakon shaƙar gurɓataccen sinadari a Kano

 

 

Akalla mutane 120 ne aka kwantar da su a asibiti bayan da su ka shaƙi warin wani gurɓataccen sinadari na masana’antu a unguwar Mundadu da ke birnin Kano.

Shedun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Juma’a lokacin da wani Saifullahi mai sana’ar gwan-gwan ke farfasa wasu ƙarafa ya ke tara wa domin sake amfani da su.

“Gurɓatacciyar Iskar ta riƙa fitowa ne daga wurin tattara ƙarafa. An fara samun matsalar ne da yammacin jiya Juma’a,” in ji wani ganau.

Mai unguwar yankin, Magaji Abdullahi ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce, “Da yammacin yau ne aka sanar da ni cewa an samu matsala a wurin da Saifullahi Muhammad yake sana’ar tattara karafa.

“An kai akalla mutane 30 asibiti. An kai wasu kuma zuwa asibitin sha-ka-tafi na Ja’en yayin da wasu kuma an kai su asibitin kwararru na Murtala Mohammed.”

Ya ce an sanar da ‘yan sanda daga sashin Ja’o’ji game da faruwar lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Abdullahi ya ce tuni aka kai mutane da dama zuwa asibitoci daban-daban domin kula da lafiyarsu.

“Kimanin 70 daga cikinsu an kai su asibitin farko na Jaen yayin da aka kai 50 asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin samun kulawa,” in ji shi.

Abdullahi ya kara da cewa kawo yanzu ba a samu asarar rai ba a lamarin.