
Rundunar ƴan sanda ta kama wani mutum mai shekaru 39 da haihuwa bisa zarginsa da yi wa matar abokinsa fyaɗe a kan gadon aurenta lokacin da shi kuma mijin ta yake ta sharar barci har da munshari a unguwar Surulere a Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Agusta, 2022 da misalin karfe 2:00 na safe.
Ana zargin kwarton ya haura gidan wanda abin ya shafa ne, kuma yayi lalata da matar ta sa ba a son ran ta ba.
Matar ta shaida wa NAN cewa ta na kwance da mijinta a kan gado ɗaya a gidansu sai ta ji ana saduwa da ita.
“Ina cikin bacci da mijina a kan gado da misalin karfe 2:00 na safe sai na ji a na saduwa da ni.
“Da farko na ɗauka mijina ne, har sai da na mika hannuna sai na ji na taɓa mijina da yake barci kusa da ni.
“Nan da nan na ta da mijina, wanda ya kunna fitila sai ya ga abokinsa yana lalata da ni.
“Har yanzu cike mu ke da mamakin yadda ya shiga gidanmu ba tare da sanin mu ba,” in ji ta.
Matar ta ce mutumin ya dora laifin abin da ya aikata a kan maye.
Jami’an ‘yan sanda na sashen Surulere ne suka kama wanda ake zargin bayan mijin ya kai ƙorafi.
Da aka tuntuɓi jami’in ’yan sanda na sashen, CSP Idowu Adedeji, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya tura NAN ga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), reshen Jihar Legas, domin jin cikakken bayani.