Home Labarai Kwastam sun kama wiwi ta kimanin Naira miliyan 20 a Kogi

Kwastam sun kama wiwi ta kimanin Naira miliyan 20 a Kogi

0
Kwastam sun kama wiwi ta kimanin Naira miliyan 20 a Kogi

Hukumar Kwastam mai kula da shiyyar Neja/Kogi, NCS, ta ce ta kama kilogiram 253.6 na tabar wiwi, wacce kudin ta ya kai Naira miliyan 20.6 a yankin Abuja zuwa Lokoja.

Shugaban hukumar ta NCS, reshen Neja/Kogi, Busayo Kadejo, ne ya bayyana hakan a jiya Talata a Minna, yayin da ya ke mika buhuhunan wiwi ɗin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, domin gudanar da bincike mai zurfi.

Kadejo ya ce tawagar ƴan sintiri na hukumar ne su ka kwace kayan.

“Mun samu amincewar da ta dace daga Babban Kwanturola-Janar na NCS, Kanar Hameed Ali mai Ritaya da ni kuma mun mika wa kwamandan NDLEA na Jihar Neja tabar wiwi ɗin da mu ka kama don ci gaba da daukar mataki,” inji shi.

Kadejo ya ci gaba da cewa, nauyin kayan ya kai kilogiram 253.6, kuma an kiyasta kudin titi ya kai Naira miliyan 20.605.