Home Labarai Kwastam ta tara harajin N935.3m a bodar Jibia-Magama tun daga 2022

Kwastam ta tara harajin N935.3m a bodar Jibia-Magama tun daga 2022

0
Kwastam ta tara harajin N935.3m a bodar Jibia-Magama tun daga 2022

Shugaban hukumar kwastam mai barin gado na yankin Katsina, Dalhatu Chedi ya bayyana cewa hukumar ta tara Naira miliyan 935.3 tun bayan sake bude iyakar Jibia-Magama daga shekarar 2022 zuwa yanzu.

Chedi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron sallama da aka shirya domin karrama shi a Katsina ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, Jibia-Magama na daya daga cikin kan iyakokin kasar guda hudu da gwamnatin tarayya ta sake budewa a watan Afrilun 2022 bayan sun dade a rufe.

A cewarsa, adadin ya zarce Naira miliyan 60.8 na Harajin da Gwamnatin Tarayya ta gindaya wa hukumar a shekarar 2022.

Ya ce, a kokarin hukumar na saukaka kasuwanci zuwa kasashen waje, ta yi hada-hadar kayayyaki da ba man fetur ba har na Naira biliyan 4.4 masu nauyin ton 69,436 na fitar da kayayyaki ta kan iyaka, karkashin shirin ‘Free-On-Board’, FOB .

“A kokarin da ake na dakile fasa kwauri, rundunar ta kuma samu kama mutane 379, inda a ka kwace kayayyaki 258 bayan cikakken bincike,” in ji shi.