
Dakarun hukumar kwastam a Najeriya ta kama wata kwantena maƙare da haramtacciyar ƙwayar a-ji-garau ta tramadol a tashar Apapa ta Jihar Legas mai darajar fiye da naira biliyan ɗaya.
Wani rahoto da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Juma’a ya ce masu kwantenar sun bayyana kayan ciki a matsayin tukunyoyi na girki, kuma suka biya biliyan 1.3 a matsayin kuɗin kayan.
Sai dai da jami’an kwastam suka buɗe kayan sai suka tarar da katan-katan na tramadol ƙunshe a cikin tukunyoyin 273.
“Kowane katan na ƙwayar na ƙunshe da kwali 50, kowane kwali na ƙunshe da fakiti 10, kowane fakiti na da ƙwaya 10,” a cewar Kwantirolan Kwastam na Apapa Malanta Yusuf.
Kwastam ta ce ta ƙwace kayan kuma ta miƙa su ga hukumar NDLEA mai yaƙi da ta’ammali da miyagiun ƙwayoyi a Najeriya.