
Daga Hassan Y.A. Malik
Wani dalibin aji biyu a karamar sakandire ya gamu da ajalin sa bayan da ya sha kwayoyin Tramadol har guda 10 a lokaci daya.
Dalibin wanda dan garin Ohafia ne da ke karamar hukumar Arochukwu a jahar Abia ya sha kwayoyin ne domin su kara masa karfi a yayin gasar tsalle tsalle da aka yi a makarantar.
Kwamandan hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA, Akindele Akingbade shi ya bayyana haka yayin da ya ke gabatar da lakca a Umuahia, babban birnin jahar, game da illolin da ke tattare da sayar da miyagun Kwayoyi, wanda masu sayar a magungna suka halarta.
A yayin da ya ke bada labarin dalibin, Akingbade ya ce jim kadan bayan ya sha magungunan ne ya ce ga garinku nan.
Akingbade wanda ya ce jahar Abia na daga cikin jahohin da shan miyagun kwayoyi ya fi kamari ya yi kira ga masu sayar da maganin da su guji sayar da su ba tare da takarda daga likita ba.