
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za’a gudanar da zaben 2023 ba tare da rikici ba.
Monguno ya ba da wannan tabbacin ne yayin ganawar sa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma shugabannin hukumomin tsaro a kasar.
Ya shawarci ƴan Nijeriya da su yi watsi da duk wani nau’i na bata-gari, labaran karya da fargaba kan yadda za a gudanar da babban zaben 2023, yana mai cewa za a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Monguno ya ce taron na da nufin duba wasu batutuwan da suka mamaye fagen siyasa da tattalin arzikin kasar a cikin makonni biyun da suka gabata, wanda ya haifar da fargaba, tashin hankali, tsoro da rashin tabbas dangane da babban zaben kasar.
“Dukkanmu mu na sane da halin da kasar nan ke ciki. Akwai bukatar in tabbatar wa ‘yan kasar nan cewa duk wani tsoro, ko tashin hankalin da muke da shi, zan so in kawar da irin wannan tunanin.
“Zaben 2023 zai gudana ne a cikin yanayi mai kyau ba tare da tashin hankali ba. Hukumomin tsaro sun yi abubuwa da yawa a cikin watanni biyun da suka gabata don tsara abubuwa.”
Monguno ya ce hukumomin tsaro na da tabbacin matakan da suka dauka.