Home Ƙasashen waje Ba laifi ba ne Musulmi ya yi bikin ‘birthday’, inji Malami a Saudiya

Ba laifi ba ne Musulmi ya yi bikin ‘birthday’, inji Malami a Saudiya

0
Ba laifi ba ne Musulmi ya yi bikin ‘birthday’, inji Malami a Saudiya

 

Wani tsohon mamba a majalisar manyan malaman Saudiyya, Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, ya ce babu wani laifi idan Musulmi ya shirya bukukuwa kamar murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko kuma ‘yan uwansa.

Saudi Gazette ta ruwaito, shehin malamin ya na mai cewa haka abin ya ke idan mutum ya yi bikin tunawa da wani abu kamar wata nasararsa, ko ta ƴaƴansa, ko samun shaidar karatu ko kammala jami’a.

A cewarsa, abin da kawai ya kamata a lura shi ne halal ne kawai amma babu haramci a kan hakan a cikin Musulunci, yana mai cewa bukukuwan na al’ada ne waɗanda ba su da alaƙa da abin da addinin ya hana.

Al-Mubarak ya ce waɗannan lamura ba sa cikin ayyukan addini da aka hana Musulmi ƙarawa ko rage wani abu daga ciki. Ba kamar faɗin Annabi SAW ba cewa: “Duk wanda ya ƙirƙiri wani abu a cikin wannan lamarin namu (Musulunci) da babu shi a cikinsa, ba za a karɓa ba,” a cewrsa.

Malamin ya jaddada cewa babu laifi idan mutum ya yi amfani da lokutan hijirar Annabi a matsayin matashiya ko alƙiblar gudanar da ayyuka a rayuwarsu ta yau da kullum.