Home Ƙasashen waje An lallashi Sergio Mattarella ya ƙara karɓar shugabancin Italiya zango na biyu duk da ba ya so

An lallashi Sergio Mattarella ya ƙara karɓar shugabancin Italiya zango na biyu duk da ba ya so

0
An lallashi Sergio Mattarella ya ƙara karɓar shugabancin Italiya zango na biyu duk da ba ya so
Majalisar dokokin Italiya ta sake zaɓar shugaba Sergio Mattarella a zangon mulki na biyu.
Sai da a ka kai gwauro, a ka kai mari sannan a ka iya shawo kan Mattarella ya yarda da ci gaba da shugabacin ƙasar.
Shugaban, mai shekaru 80 da haihuwa, wanda ake mutuntawa sosai a ƙasar, ya sha nanata cewa ba shi da sha’awar komawa mulki a zango na biyu.
Sai dai daga baya, an samu nasarar  lallasshin sa don ya ci gaba da zama bayan da ‘yan majalisar su ka kasa cimma matsaya kan wanda zai maye gurbinsa, bayan kai wa har zagaye na bakwai a zaɓe.