
Manajan Darakta na Kamfanin mai na Ƙasa, NNPC, Mele Kyari, ya bada tabbacin kawo ƙarshen layukan man da aka fara gani a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.
Kyari ya bayyana haka ne a Abuja a jiya Talata lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilai kan halin da matatun man fetur su ka shiga.
Ya tabbatar da cewa a kwai isasshen man fetur a ƙasar nan da zai biyan buƙatun al’umma.
Kyari ya ce NNPC na da jimillar lita biliyan 2.8 ta man fetur a kasar nan wanda ya isa ya biya bukatun al’ummar kasar nan na kwanaki 47 masu zuwa ba tare da shigo da wani man daga ƙasashen waje ba.
Ya danganta matsalar karancin man fetur da a ka samu a kasar nan da hutun ranar ma’aikata da hutun sallah da a ka yi a ƙasar nan, inda ya ce masu dakon man duk sun ajiye motocinsu sun tafi hutu.
A cewarsa, “mun yi duk mai yiwuwa don kada mutane su samu layika a gidajen mai kuma nan ba da jimawa ba za a kammala aikin ɓatar da kayikan a gidajen mai,” in ji shi.