Home Labarai Layin mai: Kamfanin NNPC zai ƙara jigilar mai daga motoci 70 zuwa 140 Birnin Tarayya

Layin mai: Kamfanin NNPC zai ƙara jigilar mai daga motoci 70 zuwa 140 Birnin Tarayya

0
Layin mai: Kamfanin NNPC zai ƙara jigilar mai daga motoci 70 zuwa 140 Birnin Tarayya

 

 

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya fara gudanar da ayyukansa na mako-mako tare da kudurin kawo ƙarshen layikan mai a gidajen mai daban-daban a babban birnin tarayya, Abuja.

Ta wannan kuduri, kamfanin, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, NMDPRA, sun kara kaimi wajen samar da man fetur zuwa babban birnin tarayya Abuja daga motoci 70 zuwa 140 domin yaki da layukan man da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa.

Da yake zantawa da manema labarai yayin rangadin gidajen mai a Abuja, Babban Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC na cikin ƙasa, Yemi Adetunji, ya bayyana cewa akwai isashshen man fetur a ma’ajiyar kasar nan da kwanaki 32.

“Muna da lita biliyan 1.9 na fetur wanda zai iya wuce kwanaki 32. Kamfanin NNPC na yin duk wani kokari na tabbatar da tsaron makamashi a kasar.

“Mun daidaita al’amurra a Legas. Muna aiki tare da duk masu ruwa da tsaki don ganin an shawo kan lamarin a Abuja; komai zai yi daidai nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.”

Da yake jawabi tun da fari, Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, ya bayyana cewa, an samu ci gaba da samar da man fetur daga motoci 70 zuwa 140 ne bayan amincewar da Shugaban kasa ya yi na karin rangwamen kudi ₦10 ga masu safarar man fetur a wani bangare domin samun mafita ga kalubalen samar da man fetur.