Home Ƙasashen waje Limami da matarsa da ƴaƴansa 5 sun rasu a haɗarin mota bayan kammala Ummara

Limami da matarsa da ƴaƴansa 5 sun rasu a haɗarin mota bayan kammala Ummara

0
Limami da matarsa da ƴaƴansa 5 sun rasu a haɗarin mota bayan kammala Ummara

Wani limamin a kasar Saudiyya da matarsa ​​da ‘ya’yansu biyar sun rasu a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a wani gari da ke gaɓar teku a kasar, kamar yadda jaridar Saudiyya, Okaz ta ruwaito.

Okaz ta kara da cewa, haɗarin ya afku ne a lokacin da wata motar dakon kaya da ke tafiya da gudu ta yi karo da wata mota dauke da mutanen a kan wata babbar hanya da ke kusa da birnin Al Qunfudah da ke gabar tekun kasar, inda ta kashe dukkan mutanen da ke cikin karamar motar.

Jaridar ta nakalto makusanta da abokan arziki na cewa, Sheikh Ahmed Al Basissy, limamin wani masallacin garin Al Qundudah tare da iyalansa suna dawowa daga Makkah bayan kammala aikin umrah sai motar ta yi karo da motarsu.

Labarin mummunan hatsarin ya jefa unguwar wadanda abin ya shafa cikin bakin ciki.

A halin da ake ciki kuma, ‘yan kasar Saudiyya da dama sun yi ta yada ta’aziyya ta yanar gizo tare da nuna kaduwa da rasuwar Imam da iyalansa.

Wasu masu zaman makoki sun yada faifan bidiyo da ke nuna marigayi malamin ya na gabatar da wa’azi.

Ministan harkokin addinin musulunci na Saudiyya, Abdul Latif Al Sheikh ya kuma yi ta’aziyyar rasuwar babban malamin.