Home Labarai Lokaci yayi da ya kamata likitoci da malaman Jami’a su sanya kishin kasa a zukatansu

Lokaci yayi da ya kamata likitoci da malaman Jami’a su sanya kishin kasa a zukatansu

0
Lokaci yayi da ya kamata likitoci da malaman Jami’a su sanya kishin kasa a zukatansu
Daga Ibrahim Ibb Kazaure
Zan fara da jinjinawa gwamnatin Tarayya bisa matakin da ta dauka, na hanawa tare da dakatar da dukkan likitocin gwamnati yin aiki na kansu (Private), na bayan fage wanda suke gudanarwa baya da aikinsu da gwamnati take biyansu albashi.
Zaman majalissar zartaswa ne da aka gudanar jiya laraba 11/10/2017 ta yanke wannan hukunci. Gwamnatin tace babu wani ma’aikacin gwamnati da aka bashi damar yin wani aiki na daban baicin noma.
Wannnan mataki anyi shi a lokacin da ya dace, idan aka yi la’akari da yadda harkar lafiya ke samun koma baya sakamakon irin wannan halayya da wasu likitocinmu suke dasu. Akwai rashin kishin kasa ga likitoci masu irin wannan hali, ga duk masu ziyartar asibitocin gwamnati da asibitoci masu zaman kansu zai gaskata wannan batu, yawanci suna baiwa asibitocinsu na gefe kulawa ta musamman wadda basa bada irinta a na gwamnati. Wani babban abin takilaici shine yadda  saboda son zuciya suka yarda sula karya ka’ida da sharudda na dokar ma’aikata, domin a yarjejeniyar daukar aikin gwamnati babu inda aka baiwa wani ma’aikacin gwamnati dama yaje yayi wani aikin na daban matsawar ba ritaya yayi ba.
Bugu da kari gashi suna cikin sahun gaba na yawan tafiya yajin aiki, ba tare da la’akari da irin matsayi da nauyin da yake kansu na ceton al’umma ba, hakika shima wannan rashin kishin kasa ne a bayyane.
A bangare guda kuma suma malaman jami’a kamar takwarorinsu likitoci, domin suma idan muka cire son rai muka bayyana gaskiya, za muga matsalolin su yayi kamanceceniya da likitoci, me yasa nace haka shine; su ma za ka samu lakcara daya yana koyarwa a makaranta uku ko sama da haka. Wannan ne dalili da yasa idan kaje jami’o’i dalibai ke kokowa da wasu malaman, ba don komai ba sai don wani malamin baka ganinsa sai jarrabawa tazo sannan zai zo ya koyar da kai darasin zango daya (Semester) a kwana daya ko biyu, sannan ya baku takardun karatu (Handout) yace daku mu hadu a dakin jarrabawa.
Ina kishin kasa da son cigabanta yake anan? Maganar yajin aiki kuwa ba sai nace komai ba domin ta wannan bangaren sun gwanance.
Ina kammalawa da janyo hankalin likitoci da malaman jami’o’i akan suyi amfani da ilimin da basirar da Allah ya musu su cire son zuciya daga Zukatansu su rungumi dukkan abinda zai kawo wa kasa ci gaba, su zama ‘yan kishin kasa da al’ummarta.