
Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi ne mafi girma a tarihin kasar ba.
Keyamo, Babban lauya a Nijeriya mai mukamin SAN, ya bayyana hakan a shirin safe na gidan talabijin na Arise a yau Litinin, yayin da ya ke amsa tambayoyi kan yadda Tinubu ya bayyana cewa zai dora da ga inda Buhari ya tsaya ta fuskar tattalin arziki da tsaro, da dai sauransu, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Sai dai kuma Keyamo ya yi ikirarin cewa hauhawar farashin kayayyaki ya fi yawa a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, inda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zama mataimakinsa.
“Wannan ba shine mafi girman hauhawar farashin kayayyaki ba. A shekarar 2005, a zamanin Obasanjo da Atiku, an samu hauhawar farashin kayayyaki da kashi 28 cikin 100. A karkashin Obasanjo da Atiku, mun samu mafi girma,” in ji Keyamo.
A cewar Tradingeconomics.com, da kuma wani jadawali a gidan yanar gizon Babban Bankin Najeriya, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 21.47 cikin 100 a watan Nuwamba na shekarar 2022.
PUNCH