Home Labarai Mace ta roki kotu da raba aurenta saboda ta ki jinin mijinta

Mace ta roki kotu da raba aurenta saboda ta ki jinin mijinta

0
Mace ta roki kotu da raba aurenta saboda ta ki jinin mijinta

Daga Hassan Y.A. Malik

Wata mace, Hadiza Ibrahim, ta roki kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Minna, jihar Neja, da ta warware aurenta da mijinta, domin ba ta kaunarsa ko na miskala zarratin.

Hadiza ta bayyana kotu cewa, ta gargadi mijin nata mai suna Mai-Anguwa Aliyu, tun a lokacin yana neman aurenta, da kar ya tilasta mata aurensa, domin bata sonsa bata kaunarsa, kuma idan har ya matsa aka kulla auren, to, fa ba zai ji dadin auren ba, amma ya yi kunnen uwar shegu, shi da mahaifina suka je suka daura aurena da shi ta dole.

“Ba zan ta jin so ko sha’awar mijina ba tunda ni sam bana kaunarsa, kuma duk tsawon lokacin da za a dauka wajen daidaita mu ko sulhunta mu in mun yi fada, ba zan taba sauya ra’ayina akansa ba,” Hadiza ta ce.

Daga nasa bangare, Mai-Anguwa, ya bayyana cewa shi yana matukar kaunar mai dakin nasa kuma ba ya mafarkin rabuwarsu.

Ya kuma roki kotu da ta lallashi matarsa da ta ci gaba da zama a gidansa a matsayin mai dakinsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ahmed Bima, ya shawarci ma’auratan da su bawa zaman lafiya da lumana dama ta yadda za su samu fahimtar juna a aurensu.

Bima, ya kuma gargadi jama’a, musamman maza da su kaucewa auren mace ba tare da tana so ba. Ya kara da cewa, hakan shi ke haifar da dan da bai da idanu.

Ya daga sauraren karar zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu, don bawa ma’auratan dama su sasanta.