
Daga Hassan Y.A. Malik
Wata tsohuwa ‘yar asalin kasar Japan, wacce ake kyautata zaton ita ta fi kowa tsufa a duniya, ta riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito.
Tsohuwar mai suna Nabi Tajima, wacce aka haifa a ranar 4 ga watan Agustan 1900, ta rasu ne da misalin karfe 8:00 na daren Asabar a asibiti.
Kafafen yada labaran kasar Japan sun rawaito cewa Tajima ita ta kasance macen da ta fi tsufa tun 2015 bayan rasuwar Violet Brown ‘yar kasar Jamaica.
Kundin Guiness World Records shi ya gano cewa Tajima ta fi kowa tsufa bayan da binciken shi ya kasa samo macen da ta fi ta shekaru a fadin duniya.