Home Labarai ‘Maganar da Sarki Sanusi ya yi kan sauya fasalin Naira ba da El-Rufai ya ke ba’

‘Maganar da Sarki Sanusi ya yi kan sauya fasalin Naira ba da El-Rufai ya ke ba’

0
‘Maganar da Sarki Sanusi ya yi kan sauya fasalin Naira ba da El-Rufai ya ke ba’

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, wanda tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll ya bayyana a ciki kuma ya ke nuna goyon bayan manufar sauyin kuɗi a Nijeriya ba na yanzu ba ne.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a kwanan nan ne faifan bidiyo ya bayyana, inda a ciki Sarki Sanusi ya nuna goyon bayansa ga Babban Bankin Ƙasa, CBN kan sauyin kuɗi.

A bidiyon, Sanusi ya ce manufar ta yi daidai domin za ta hana ƴan siyasa sayen kuri’a da kuma baiwa hukumar zabe da jami’an tsaro kuɗi domin su murɗe zaɓe.

Sai dai kuma tuni gwamnonin APC su ka nuna adawar su ga manufar ta babban bankin tarayya, musamman gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, wanda ya shige gaba wajen maka gwamnatin tarayya a Kotun Ƙoli a kan manufar ta CBN.

Wannan jarida ta tuna cewa El-Rufai abokin Sanusi ne sosai, inda hakan ya sanya wasu ke ganin kamar tsohon sarkin da shi (El-Rufai) ya ke.

Sai dai kuma wani makusancin Sanusi da ya nemi da a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar nan cewa “ko kusa ko alama Sanusi ba da El-Rufai ya ke ba.”

A cewar makusancin, Sanusi ya yi maganar ne ba don mutum guda ba, musamman ma El-Rufai, inda ya ƙara da cewa hasali ma faifan bidiyon tsoho ne.

Ya ce faifan bidiyo ɗin ma an dauke shi ne tun ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba, 2023, inda ya ƙara da cewa “ko kaɗan ba da El-Rufai Mai Martaba ya ke ba. Kowa ya san irin amintakar da ke tsakanin Sarki Sanusi da El-Rufai, ta yaya zai fito bainar jama’a ya faɗi haka a kan sa?”

“Ai idan ma gaskiyar zai faɗa masa, ba zai fito bainar jama’a ya faɗa ba, sai dai shi da shi ya faɗa masa,” in ji makusancin.

Ya ce an dauki ma bidiyo ɗin ne a yayin karatun littafin Madarijil Salkhin da sarki ya saba gudanarwa.