
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce dole ne a haɗa ƙarfi da ƙarfe a magance aiyukan ƴan ta’adda masu fashin daji a Arewacin Nijeriya Kafin shekarar 2023.
Masari ya bada wannan tabbacin ne a yayin da ya ke sanya hannu a ƙudurin kasafin kuɗi na 2022 a ranar Laraba a gidan gwamnati.
Gwamnan ya ci alwashin cewa babu gudu babu ja da baya a yaƙi da ƴan fashin daji.
A cewar Masari, ƴan fashin dajin sanannu ne a garuruwansu, inda ya ƙara da cewa babu yadda za a yi ɓatagari su riƙa riƙe bindiga kuma a ce al’umma ba za su kare kan su ba.
“Dole ne mu tashi tsaye mu yaƙi ƴan fashin daji sabo da shaidanu ne kuma wakilan shaidan ne. Ba gudu ba ja da baya a yaƙin nan.
“Mun karbi mulki a cikin haɗarin rashin tsaro a 2015 kuma in Allah Ya yarda ba za mu mika mulki a cikin wannan yanayi na rashin tsaro ba,” in ji Masari.
Gwamnan ya ƙara da cewa hanya ɗaya ta ganawa da ƴan ta’adda ita ce a nuna musu cewa a shirye a ke da a gama da su da kuma cewa a shirye a ke a kare al’umma.