Home Labarai Magidanci ya yi wa agolarsa ƴar shekara 15 ciki a Ekiti

Magidanci ya yi wa agolarsa ƴar shekara 15 ciki a Ekiti

0
Magidanci ya yi wa agolarsa ƴar shekara 15 ciki a Ekiti

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai suna Ojo Babatunde bisa zarginsa da yin lalata da agolarsa ƴar shekara 15 da haihuwa.

DSP Sunday Abutu, mai magana da yawun rundunar, ya tabbatar da kama shi a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Ado-Ekiti.

Ya ce Sashin Walwalar Al’umma na sashen binciken manyan laifuka na rundunar ne ya kama Babatunde.

“An kama wanda ake zargin ne a lamba 15, titin Edugbe, Obadore, Omuo-Ekiti a Ƙaramar huk5umar Ekiti-ta-Gabas ta jihar.

“yarinyar da abin ya shafa, wacce tuni tana da ciki wata hudu, ta yi ikirarin cewa Babatunden mijin mahaifiyarta ne.

“Ta ce Abutu ya fara haike mata ne tun lokacin da mahaifiyarta ta haihu kuma ta kwashe kusan makonni uku a asibiti.