
Ɗaruruwan magoya baya, da su ka haɗa da matasa da gungun mata ne a yau Juma’a su ka yi tsinke a ofishin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.
Magoya bayan, wandanda su ka cika ofishin nasa ɗauke da kwalaye masu ɗauke da sakonni daban-daban, sun yi kira a gare shi da ya fito takarar shugabancin ƙasa a 2023.
Tun misalin ƙarfe 8 na safe ne dai magoya bayan su ka isa ofishin na Jonathan ɗauke da kayan kida, inda su ke ta rera wakoki na goyon baya iri-iri.
Sun nuna takaicin su cewa tun da Jonathan ya bar mulki, yunwa, talauci, rashin tsaro da rashin aikin yi sun yi wa ƙasar katutu.
Masoyan na Jonathan sun ce al’ummar ƙasa, maza da mata sun zama almajirai sabo da irin tsauraran manufofin gwamnti mai ci.