
Daga Ibrahim Abdul
Yanzu haka wata sabuwar dambarwa ta sake ɓarkewa a jam’iyar APC reshen jihar Taraba a tsakanin ɓangarori biyu na shugabanin jam’iyar da ke da alaƙa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ’yan ɓangaren dake tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugabanin jam’iyar APC a jihar Taraban dake tare da bangaren ministar harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan ne dai suka soma jangwalota, inda suka bukaci tsohon shugaban jam’iyar wanda yanzu ya zama jakada, wato Ambassada Hassan Jika Arɗo, da ya hanzarta ya maido da mota ƙirar Prado Jeep da Atiku ya ba shi a watannin baya.
Ambasada Arɗo dai da tuni suka raba gari da Minista Aisha Alhassan saboda karkatar da ta yi wajen Atiku.
A wata wasiƙa da suka aikewa tsohon shugaban jam’iyar, ’yan tsagin Minista Aisha na iƙirarin cewa Atiku ne ya buƙaci a maido da motar, batun da yan ɓangaren su Jika Ardon, wato yan ‘APC Integrity’ dake goyon bayan shugaba Buhari ke cewa ba zata saɓu ba, wai bindiga a ruwa.
A ganawarsu da manema labarai ’yan ‘APC Integrity’ sun yi tir da wannan batu, inda Alhaji Iliyasu Mu’azu ke cewa ai ba’a taɓa yin kyauta a ƙwace ba.
Alhaji Iliyasu ya ce, “Abun takaici ne wai Atiku zai yi kyauta, amma yace wai a komar masa da motar. Ni ina ganin wannan abin dubawa ne.
“Ita dai ministar so take kawai ta ruguza APC kafin ta fice, tunda suna hanyar komawa PDP ita da uban gidanta Atiku. Mu kam sai dai mu ce Allah ya raka taki gona.
“To amma idan har Atiku ya ƙwace motar, to mu a shirye muke mu sayawa Arɗo wata motar,” a lafazin Alhaji Mu’azu.
To sai dai kuma a martaninsu, shugabanin jam’iyar APC a jihar sun musanta zargin cewa ƙwatar motar na da nasaba da dambarwar Buhari da Atiku.
Alhaji Abdullahi Ade wanda ke cikin shugabanin jam’iyar a ɓangaren ministar matan ya ce sun ɗau wannan mataki ne don komowa da jam’iyya motar.
“A’a, ai motar jam’iya aka baiwa ba wani ba. Kuma tunda yanzu ya zama jakadan Najeriya a wata kasar, shi yasa muka rubuta masa takarda ya komo da motar tunda bada ita zai tafi ba.
“Kuma muna da takardar da mai girma tsohon mataimakin shugaban kasa ya turo na a maidowa jam’iya motar ta,” a cewar Ade, wanda shi ne shugaban matasa na jam’iyar APC a jihar.
Da yake maida martani a kan taƙaddamar, Ambassada Ardo ya ce shi kyauta aka bashi ba ta jam’iya bace.
“Lokacin da minister Aisha ta zo da motar ai kyauta tace, kuma babu takardar shaidar cewa jam’iya aka baiwa motar.
“I gaskiya ne sun aiko mun wasiƙu biyu, ta farko ɗauke da kwanan wata 9 ga Satumba, kuma da sa hannun Mr Solomon Jadana mataimakin shugaban jam’iyar na shiya wanda yanzu ke iƙirarin kujerar sakataren jam’iyar.
“Sauran waɗanda suke cewa sune ’yan kwamitin ƙwatar motar sun haɗa da wani da ke iƙirarin cewa wai shi lauya ne, wato Haladu Yakubu, da Sani Mamman Posa da Aliyu Umar Bali da kuma Godwin Villana.
“Haka nan wasiƙar ta biyu, mai kwanan wata 27 ga watan Satumbar 2017, ita ma suna wai cewa ta fito ne daga tsohon mataimakin shugaban kasan Atiku Abubakar kuma tana ɗauke da sahannun Abdullahi Nyako,” a cewar Ambassada Hassan Jika Ardo.