Home Siyasa Magoya bayan Wike sun roƙi kotu da ta ƙwace takarar Atiku

Magoya bayan Wike sun roƙi kotu da ta ƙwace takarar Atiku

0
Magoya bayan Wike sun roƙi kotu da ta ƙwace takarar Atiku

 

 

 

Magoya bayan Nyesom Wike sun maka Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a kotu kan yadda zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP ya kasance.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Newgent Ekamon, ƙusa a jam’iyyar PDP, ya roki kotu da ta umarci INEC ta cire sunan Atiku daga jerin sunayen ƴan takara na zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A tuna cewa, a watan Mayu, Wike ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a hannun Atiku, bayan Tambuwal ya janye wa Atikun, sannan ya umarci magoya bayansa da su zaɓe shi.

Yayin da Atiku ya samu kuri’u 371 ya zama dan takarar PDP bayan ya doke Wike, wanda ya samu kuri’u 237 ya zo na biyu.

Sakamakon zaben fidda-gwanin ne dai ya haifar da rikici a cikin jam’iyyar.

A wata ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022, Ekamon da sauran magoys bayan Wike, sun bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta tabbatar ko bada kuri’un da Tambuwal ya yi ga Atiku ya halasta.

Sun roki kotun da ta bayyana cewa PDP ta yi kuskure ta sanya kuri’un Tambuwal ga tsohon mataimakin shugaban kasa.

Sun kuma roƙi kotun da ta ayyana Wike a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda-gwani na PDP da s ka yi a ranar 28 da 29 na Mayu.