
Ƴan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum mai shekaru 46, Olusegun Oluwole bisa zarginsa da lalata ƴarsa, mai shekaru 17 da haihuwa.
Jami’an vigilante na jihar Ogun, So-Safe Corps,’ ne su ka cafke wanda ake zargin tare da miƙa shi ga ƴan sanda.
An ce da misalin karfe 11:30 na dare ya kama ƴar sa ya yi mata fyaɗe, inda ya yi barazanar kashe ta idan ta ki yarda da shi.
Kakakin rundunar ƴan sandan, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar jiya.
Ya kuma tabbatar da cewa mahaifin zai fuskanci hukunci bayan kammala bincike.