Home Labarai Mahaifi ya tsere da raunuka a jiki bayan da ƴan bindiga su kai garkuwa da ɗansa ɗan shekara 4

Mahaifi ya tsere da raunuka a jiki bayan da ƴan bindiga su kai garkuwa da ɗansa ɗan shekara 4

0
Mahaifi ya tsere da raunuka a jiki bayan da ƴan bindiga su kai garkuwa da ɗansa ɗan shekara 4

 

 

 

 

An yi garkuwa da wani yaro ɗan shekara huɗu mai suna Oluwadarasimi Omojola a kan hanyar Itaji/Ijelu Ekiti a Ƙaramar Hukumar Oye ta jihar Ekiti.

Mai sarautar gargajiya ta Owajumu na Omu Ekiti, Oba Gabriel Ogundeyi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe shida na yamma.

Sarkin ya ce yaron yana dawowa daga Ayede Ekiti tare da mahaifinsa, Boluwaji Omojola, wanda ya yi nasarar tserewa bayan ya samu raunuka mai tsanani daga wadanda suka yi garkuwa da su, kuma a halin yanzu yana samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Oba Ogundeyi ya ce tun daga lokacin ne aka tattara jami’an tsaro da mafarautan yankin domin su bi bayan masu garkuwa da mutanen domin ceto yaron.