
Ladi Bako, matar gwamnan jihar Kano na farko, Audu Bako, ta rasu.
Marigayiyar ta rasu ta na da shekaru 93 a duniya.
Ƴar marigayiyar, Zainab Bako ce ta tabbatar wa DAILY NIGERIAN labarin rasuwar a yau Laraba, inda ta ce ta rasu ne a asibitin Prime Specialist da ke Kano bayan doguwar jinya.
Ta kara da cewa za a yi jana’izar ta ne a fadar sarki, Kofar Kudu a Kano.
An nada mijin marigayiyar, Audu Bako, gwamnan soja a tsohuwar jihar Kano daga Mayun 1967 zuwa Yulin 1975.
Ya kawo ci gaba iri-iri da kuma gina ma’aikatu a fadin jihar.