Home Labarai Mai-ɗakin El-Rufa’i ta roƙi Tinubu da ya naɗa mata matsayin AGF da SGF a gwamnatinsa

Mai-ɗakin El-Rufa’i ta roƙi Tinubu da ya naɗa mata matsayin AGF da SGF a gwamnatinsa

0
Mai-ɗakin El-Rufa’i ta roƙi Tinubu da ya naɗa mata matsayin AGF da SGF a gwamnatinsa

 

 

 

 

Asiya El-Rufai, uwargidan gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ta bukaci a baiwa mata mukamin Antoni-Janar na Taryya, AGF, a gwamnatin Bola Tinubu.

Uwargidan gwamnan ta bayyana haka ne a wajen bikin taya Bola Tinubu murna ɓangaren mata kwararru na jam’iyyar APC, su ka gudanar a yau Alhamis a Abuja.

Ta kara da cewa mukamin Ministan Lafiya, Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Mataimakin Shugaban Ma’aikata, DCoS, ga Shugaban kasa, ya kamata a kebe su ga mata.

“Muna son a ba wa mace SGF, ba a taba yi ba, muna son Ministan Lafiya da akalla Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa a ba mata.

“Shugaban mu, Tinubu ya damu matuka da irin rawar da mata za su taka wajen gina kasa, kuma ina mai tabbatar mana da cewa kashi 35 cikin 100 na tabbacin da muka yi ta kokawa a kai.

“Mu masu warware matsaloli ne ba manazarta ba. Dole ne mu jajirce mu cire duk wani son rai. Ya kamata manufar mu tazama guda ɗaya, wato mu tabbatar da nasara ga jam’iyyarmu,” in ji ta