
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta bada tallafin Naira Miliyan 500 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Oluremi ta sanar da bada tallafin ne a ziyarar jaje da ta kai ga Gwamna Babagana Zulum a jiya Laraba a birnin Maiduguri.
Matar shugaban kasar, wacce ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima wacce ta gabatar da tallafin ta Naira Miliyan 500 ga wadanda abin ya shafa.
Ta yabawa gwamnatin jihar bisa kokarin ta a kowanne mataki.
Da yake jawabi, Gwamna Zulum ya yaba da tallafin, inda ya kara da cewa shirin RHI ya tallafawa mata da dama da masu karamin karfi a jihar.
Ya ce, shima shugaban kasa Tinubu ya ziyarci Maiduguri a ranar Litinin domin jajantawa al’ummar jihar kan iftila’in.